44 Kullum zan yi biyayya da dokarka har abada abadin!
45 Zan rayu da cikakken 'yanci,Gama na yi ƙoƙari in kiyaye ka'idodinka.
46 Zan hurta umarnanka ga sarakuna,Ba kuwa zan ji kunya ba.
47 Ina murna in yi biyayya da umarnanka,Saboda in ƙaunarsu.
48 Ina girmama umarnanka, ina kuwa ƙaunarsu,Zan yi ta tunani a kan koyarwarka.
49 Ka tuna da alkawarin da ka yi mini, ni bawanka,Ka ƙarfafa zuciyata.
50 Ko ina shan wahala, ana ta'azantar da ni,Saboda alkawarinka yana rayar da ni.