47 Ina murna in yi biyayya da umarnanka,Saboda in ƙaunarsu.
48 Ina girmama umarnanka, ina kuwa ƙaunarsu,Zan yi ta tunani a kan koyarwarka.
49 Ka tuna da alkawarin da ka yi mini, ni bawanka,Ka ƙarfafa zuciyata.
50 Ko ina shan wahala, ana ta'azantar da ni,Saboda alkawarinka yana rayar da ni.
51 Masu girmankai suna raina ni,Amma ban rabu da dokarka ba.
52 Na tuna da koyarwar da ka yi mini a dā,Sukan kuwa ta'azantar da ni, ya Ubangiji.
53 Haushi ya kama ni sosai,Sa'ad da na ga mugaye suna keta dokarka.