7 Zan yabe ka da tsattsarkar zuciya,A sa'ad da na fahimci ka'idodinka masu adalci.
8 Zan yi biyayya da dokokinka,Ko kusa kada ka kashe ni!
9 Ƙaƙa saurayi zai kiyaye ransa da tsarki?Sai ta wurin biyayya da umarnanka.
10 Da zuciya ɗaya nake ƙoƙarin bauta maka,Ka kiyaye ni daga rashin biyayya da umarnanka!
11 Na riƙe maganarka a zuciyata,Don kada in yi maka zunubi.
12 Ina yabonka, Ya Ubangiji,Ka koya mini ka'idodinka!
13 Zan ta da murya,In maimaita dukan dokokin da ka bayar.