76 Ka sa madawwamiyar ƙaunarka ta ta'azantar da ni,Kamar yadda ka alkawarta mini, ni bawanka.
77 Ka yi mini jinƙai, zan rayu,Saboda ina murna da dokarka.
78 Ka kunyatar da masu girmankaiSaboda sun ba da shaidar zur a kaina,Amma ni, zan yi tunani a kan ka'idodinka.
79 Ka sa waɗanda suke tsoronka su zo gare ni,Da waɗanda suka san umarnanka.
80 Ka sa in yi cikakkiyar biyayya da umarnanka,Sa'an nan zan tsere wa shan kunyar faɗuwa.
81 Na tafke, ya Ubangiji, jira nake ka cece ni,Na dogara ga maganarka.
82 Idanuna sun gaji da zuba ido ga alkawarinka.Roƙo nake, “Sai yaushe za ka taimake ni?”