85 Masu girmankai, waɗanda ba su biyayya da dokarka,Sun haƙa wushefe don su kama ni.
86 Umarnanka duka, abin dogara ne,Mutane suna tsananta mini da ƙarairayi,Ka taimake ni!
87 Sun kusa ci wa burinsu na su kashe ni,Amma ban raina ka'idodinka ba.
88 Saboda madawwamiyar ƙaunarka, ka yi mini alheri,Domin in yi biyayya da dokokinka.
89 Maganarka tabbatacciya ce, ya Ubangiji,A kafe take a Sama.
90 Amincinka ya tabbata har abada,Ka kafa duniya a inda take, tana nan kuwa a wurin.
91 Dukan abubuwa suna nan har wa yau saboda umarninka,Domin su duka bayinka ne.