96 Na koya cewa ba wani abu da yake cikakke,Amma umarninka ba shi da iyaka.
97 Ga yadda nake ƙaunar dokarka!Ina ta tunani a kanta dukan yini.
98 Umarninka yana tare da ni a kowane lokaci,Ya sa ni in yi hikima fiye da dukan maƙiyana.
99 Ganewata ta fi ta dukan malamaina,Saboda ina ta tunani a kan koyarwarka.
100 Na fi tsofaffi hikima,Saboda ina biyayya da umarnanka.
101 Nakan guje wa halin muguntaSaboda ina so in yi biyayya da maganarka.
102 Ban raina koyarwarka baSaboda kai ne ka koya mini.