1 Sa'ad da Ubangiji ya komar da mu cikin Sihiyona,Sai abin ya zama kamar mafarki!
2 Muka kece da dariya, muka raira waƙa don farin ciki,Sa'an nan sai sauran al'umma suka ambace mu, suka ce,“Ubangiji ya yi manyan al'amura masu girma, sabili da su!”
3 Hakika ya aikata manyan al'amura sabili da mu,Mun kuwa yi farin ciki ƙwarai!
4 Ya Ubangiji, ka komar da mu ƙasarmuKamar yadda ruwan da kake yi yakan koma cikin busassun koguna,