15 Zan tanada wa Sihiyona dukan abin da take bukata a yalwace,Zan ƙosar da matalautanta da abinci.
16 Zan sa firistocinta su yi shela,Cewa ina yin ceto,Jama'ata kuma za su raira waƙa,Suna sowa don farin ciki.
17 A nan ne zan naɗa ɗaya daga cikin zuriyar DawudaYake zama babban sarki,A nan ne kuma zan wanzar daMulkin zaɓaɓɓen sarkina.
18 Zan sa maƙiyansa su sha kunya,Amma mulkinsa zai arzuta.Ya kuma kahu.”