3 “Ba zan tafi gida ko in kwanta ba,
4 Ba zan huta, ko in yi barci ba,
5 Sai sa'ad da na shirya wa Ubangiji wuri,Wato Haikali domin Maɗaukaki, Allah na Isra'ila.”
6 Mun ji labari akwatin alkawari yana Baitalami,Amma muka same shi a kurmi.
7 Muka ce, “Bari mu tafi Haikalin Ubangiji,Mu yi sujada a gaban kursiyinsa!”
8 Ka zo wurin hutawarka, ya Ubangiji,Tare da akwatin alkawari,Alama ce ta ikonka.
9 Ka suturta firistoci da adalci,Ka sa dukan jama'arka su yi sowa ta farin ciki!