1 Ku yabi Ubangiji!Ku yabi sunansa, ku bayin Ubangiji,
2 Ku da kuke tsaye a Haikalin Ubangiji,A wuri mai tsarki na Allahnmu.
3 Ku yabi Ubangiji, domin nagari ne shi,Ku raira yabbai ga sunansa, domin shi mai alheri ne.
4 Ya zaɓar wa kansa Yakubu,Jama'ar Isra'ila kuwa tasa ce.
5 Na sani Ubangijinmu mai girma ne,Ya fi dukan alloli girma.
6 Yana aikata dukan abin da ya ga dama a Sama ko a duniya,A tekuna, da kuma zurfafan da suke ƙarƙas.