10 Ya hallakar da sauran al'umma masu yawa,Ya karkashe sarakuna masu iko, wato
11 Sihon, Sarkin Amoriyawa, da Og, Sarkin Bashan,Da dukan sarakunan Kan'ana.
12 Ya ba da ƙasarsu ga jama'arsa,Ya ba da ita ga Isra'ila.
13 Ya Ubangiji, kullayaumi mutane za su sani kai ne Allah,Dukan tsararraki za su tuna da kai.
14 Ubangiji zai ji juyayin mutanensa,Zai 'yantar da bayinsa.
15 Gumakan al'ummai, da azurfa da zinariya aka yi su,Hannuwan mutane ne suka siffata su.
16 Suna da bakuna, amma ba sa magana,Da idanu, amma ba sa gani.