4 Ya zaɓar wa kansa Yakubu,Jama'ar Isra'ila kuwa tasa ce.
5 Na sani Ubangijinmu mai girma ne,Ya fi dukan alloli girma.
6 Yana aikata dukan abin da ya ga dama a Sama ko a duniya,A tekuna, da kuma zurfafan da suke ƙarƙas.
7 Yakan kawo gizagizan hadiri daga bangayen duniya,Yakan yi walƙiya domin hadura,Yakan fito da iska daga cikin taskarsa.
8 A Masar ne ya karkashe 'ya'yan fari na mutane da na dabbobi.
9 A can ne ya aikata mu'ujizai da al'ajabai,Domin ya hukunta Fir'auna da dukan hukumar ƙasarsa.
10 Ya hallakar da sauran al'umma masu yawa,Ya karkashe sarakuna masu iko, wato