1 Ku gode wa Ubangiji domin shi mai alheri ne,Gama ƙaunarsa madawwamiya ce.
2 Ku gode wa Allahn da ya fi dukan alloli girma,Gama ƙaunarsa madawwamiya ce.
3 Ku gode wa Ubangijin dukan iyayengiji,Gama ƙaunarsa madawwamiya ce.
4 Shi kaɗai ne yake aikata mu'ujizai masu girma,Gama ƙaunarsa madawwamiya ce.
5 Ta wurin hikimarsa ya halicci sammai,Gama ƙaunarsa madawwamiya ce.
6 Ya kafa duniya a bisa kan ruwa mai zurfi,Gama ƙaunarsa madawwamiya ce.
7 Shi ne ya halicci rana da wata,Gama ƙaunarsa madawwamiya ce,