16 Ya bi da jama'arsa cikin hamada,Gama ƙaunarsa madawwamiya ce.
17 Ya karkashe sarakuna masu iko,Gama ƙaunarsa madawwamiya ce.
18 Ya karkashe shahararrun sarakuna,Gama ƙaunarsa madawwamiya ce.
19 Ya kashe Sihon, Sarkin Amoriyawa,Gama ƙaunarsa madawwamiya ce.
20 Ya kashe Og, Sarkin Bashan,Gama ƙaunarsa madawwamiya ce.
21 Ya ba da ƙasarsu ga jama'arsa,Gama ƙaunarsa madawwamiya ce.
22 Ya ba da ita ga bawansa Isra'ila,Gama ƙaunarsa madawwamiya ce.