4 Shi kaɗai ne yake aikata mu'ujizai masu girma,Gama ƙaunarsa madawwamiya ce.
5 Ta wurin hikimarsa ya halicci sammai,Gama ƙaunarsa madawwamiya ce.
6 Ya kafa duniya a bisa kan ruwa mai zurfi,Gama ƙaunarsa madawwamiya ce.
7 Shi ne ya halicci rana da wata,Gama ƙaunarsa madawwamiya ce,
8 Rana don ta yi mulkin yini,Gama ƙaunarsa madawwamiya ce,
9 Wata da taurari kuwa don su yi mulkin dare,Gama ƙaunarsa madawwamiya ce.
10 Shi ya karkashe 'ya'yan fari maza, na Masarawa,Gama ƙaunarsa madawwamiya ce.