5 Ta wurin hikimarsa ya halicci sammai,Gama ƙaunarsa madawwamiya ce.
6 Ya kafa duniya a bisa kan ruwa mai zurfi,Gama ƙaunarsa madawwamiya ce.
7 Shi ne ya halicci rana da wata,Gama ƙaunarsa madawwamiya ce,
8 Rana don ta yi mulkin yini,Gama ƙaunarsa madawwamiya ce,
9 Wata da taurari kuwa don su yi mulkin dare,Gama ƙaunarsa madawwamiya ce.
10 Shi ya karkashe 'ya'yan fari maza, na Masarawa,Gama ƙaunarsa madawwamiya ce.
11 Shi ya fito da jama'ar Isra'ila daga cikin Masar,Gama ƙaunarsa madawwamiya ce.