1 A bakin kogunan BabilaMuka zauna muka yi ta kuka,Sa'ad da muka tuna da Sihiyona.
2 A rassan itatuwan wardi da suke kusa da muMuka rataye garayunmu.
3 Waɗanda suka kama mu suka sa mu mu yi waƙa,Suka ce mana, “Ku yi mana shagaliDa waƙar da aka raira wa Sihiyona!”
4 Kaƙa za mu raira waƙar UbangijiA baƙuwar ƙasa?