21 Ya Ubangiji, ga yadda nake ƙin waɗanda suke ƙinka,Da yadda nake raina waɗanda suke tayar maka!
22 Ƙiyayyar da nake yi musu ta kai intaha,Na ɗauke su, su abokan gābana ne.
23 Jarraba ni, ya Allah, ka san tunanina,Gwada ni, ka gane damuwata.
24 Ka bincike, ko akwai wani rashin gaskiya a gare ni,Ka bi da ni a madawwamiyar hanya.