4 Tun kafin in yi maganaKa riga ka san abin da zan faɗa.
5 Kana kewaye da ni a kowane sashe,Ka kiyaye ni da ikonka.
6 Yadda ka san ni ya fi ƙarfin magana,Ya yi mini zurfi, ya fi ƙarfin ganewata.
7 Ina zan tafi in tsere wa Ruhunka?Ina zan gudu in tsere maka?
8 Idan na hau cikin samaniya kana can,In na kwanta a lahira kana can,
9 In na tashi sama, na tafi, na wuce gabas,Ko kuma na zauna a can yamma da nisa,
10 Kana can domin ka bi da ni,Kana can domin ka taimake ni.