1 Ka cece ni daga mugaye, ya Ubangiji,Ka kiyaye ni daga mutane masu hargitsi.
2 Kullum suna shirya mugunta,Kullum suna kawo tashin hankali.
3 Harsunansu kamar macizai masu zafin dafi,Kalmominsu kuwa kamar dafin gamsheƙa ne.
4 Ka tsare ni daga ikon masu mugunta, ya Ubangiji,Ka kiyaye ni daga masu tashin hankali,Waɗanda suke shirya fāɗuwata.
5 Masu girmankai sun kafa mini tarko,Sun shimfiɗa ragar igiya,Sun kuma kakkafa tarkuna a hanya don su kama ni.