2 Kullum suna shirya mugunta,Kullum suna kawo tashin hankali.
3 Harsunansu kamar macizai masu zafin dafi,Kalmominsu kuwa kamar dafin gamsheƙa ne.
4 Ka tsare ni daga ikon masu mugunta, ya Ubangiji,Ka kiyaye ni daga masu tashin hankali,Waɗanda suke shirya fāɗuwata.
5 Masu girmankai sun kafa mini tarko,Sun shimfiɗa ragar igiya,Sun kuma kakkafa tarkuna a hanya don su kama ni.
6 Na ce wa Ubangiji, “Kai ne Allahna.Ka ji kukana na neman taimako, ya Ubangiji!
7 Ya Ubangiji, Allahna, Mai Cetona, mai ƙarfi,Kā kiyaye ni cikin yaƙi.
8 Ya Ubangiji, kada ka biya wa mugaye burinsu,Kada ka bar mugayen dabaru su yi nasara!