5 Masu girmankai sun kafa mini tarko,Sun shimfiɗa ragar igiya,Sun kuma kakkafa tarkuna a hanya don su kama ni.
6 Na ce wa Ubangiji, “Kai ne Allahna.Ka ji kukana na neman taimako, ya Ubangiji!
7 Ya Ubangiji, Allahna, Mai Cetona, mai ƙarfi,Kā kiyaye ni cikin yaƙi.
8 Ya Ubangiji, kada ka biya wa mugaye burinsu,Kada ka bar mugayen dabaru su yi nasara!
9 “Kada ka bar maƙiyana su sami nasara,Ka sa kashedin da suke yi mini yă koma kansu.
10 Ka sa garwashin wuta yă zubo a kansu,Ka sa a jefa su a rami, kada su ƙara fita.
11 Ka sa waɗanda suke saran waɗansu a ƙaryace,Kada su yi nasara.Ka sa mugunta ta hallaka mutumin da yake ta da zaune tsaye.”