4 Shi kamar hucin iska yake,Kwanakinsa kuwa kamar inuwa mai wucewa ne.
5 Ya Ubangiji, ka kware sararin sama, ka sauko,Ka taɓa duwatsu, don su tuƙaƙo da hayaƙi.
6 Ka aiko da walƙiyar tsawa ta warwatsa maƙiyanka,Ka harba kibanka, ka sa su sheƙa a guje!
7 Ka sunkuyo daga Sama,Ka tsamo ni daga cikin ruwa mai zurfi, ka cece ni,Ka cece ni daga ikon baƙi,
8 Waɗanda ba su taɓa faɗar gaskiya ba,Sukan yi rantsuwar ƙarya.
9 Zan raira maka sabuwar waƙa, ya Allah,Zan kaɗa garaya in raira maka waƙa.
10 Ka ba sarakuna nasara,Ka kuma ceci bawanka Dawuda.