11 Za su yi maganar darajar mulkinka,Su ba da labarin ikonka,
12 Domin haka dukan mutane za su san manyan ayyukanka,Da kuma darajar ɗaukakar mulkinka.
13 Mulkinka, madawwamin mulki ne,Sarki ne kai har abada.
14 Ubangiji, yakan taimaki dukan waɗanda yake shan wahala,Yakan ta da waɗanda aka wulakanta.
15 Dukan masu rai suna sa zuciya gare shi,Yana ba su abinci a lokacin da suke bukata,
16 Yana kuwa ba su isasshe,Yakan biya bukatarsu duka.
17 Ubangiji mai adalci ne a abin da yake yi duka,Mai jinƙai ne a ayyukansa duka.