18 Yana kusa da dukan waɗanda suke kira gare shi,Waɗanda suke kiransa da zuciya ɗaya.
19 Yakan biya bukatar dukan waɗanda suke tsoronsa,Yakan ji kukansu, ya cece su.
20 Yakan kiyaye dukan waɗanda suke ƙaunarsa,Amma zai hallaka mugaye duka.
21 A kullum zan yabi Ubangiji,Bari talikai duka su yabi sunansa mai tsarki har abada!