4 Za a yabi abin da ka aikata daga tsara zuwa tsara,Za su yi shelar manya manyan ayyukanka.
5 Mutane za su yi magana a kan darajarka da ɗaukakarka,Ni kuwa zan yi ta tunani a kan ayyukanka masu banmamaki.
6 Mutane za su yi magana a kan manya manyan ayyukanka,Ni kuwa zan yi shelar girmanka.
7 Za su ba da labarin girmanka duka,Su kuma raira waƙa a kan alherinka.
8 Ubangiji mai ƙauna ne, mai jinƙai, mai jinkirin fushi,Cike da madawwamiyar ƙauna.
9 Shi mai alheri ne ga kowa,Yana juyayin dukan abin da ya halitta.
10 Ya Ubangiji, talikanka duka za su yabe ka,Jama'arka kuma za su yi maka godiya!