1 Yabo ya tabbata ga Ubangiji!Ka yabi Ubanigji, ya raina!
2 Zan yabe shi muddin raina.Zan raira waƙa ga Allahna dukan kwanakina.
3 Kada ka dogara ga shugabanni,Ko kowane mutum da ba zai iya cetonka ba.
4 Sa'ad da suka mutu sai su koma turɓaya,A wannan rana dukan shirye-shiryensu sun ƙare.
5 Mai farin ciki ne mutumin da Allah na Yakubu ne yake taimakonsa,Yana kuma dogara ga Ubangiji Allahnsa,
6 Wanda ya halicci sama, da duniya, da teku,Da dukan abin da yake cikinsu.Kullum yakan cika alkawaransa.