6 Wanda ya halicci sama, da duniya, da teku,Da dukan abin da yake cikinsu.Kullum yakan cika alkawaransa.
7 A yanke shari'arsa yakan ba wanda aka zalunta gaskiya.Yana ba da abinci ga mayunwata.Ubangiji yakan kuɓutar da ɗaurarru.
8 Yakan ba makafi ganin gari.Yakan ɗaukaka waɗanda aka wulakanta.Yana ƙaunar jama'arsa, adalai.
9 Yakan kiyaye baƙi waɗanda suke zaune a ƙasar.Yakan taimaki gwauraye, wato matan da mazansu suka mutu, da marayu.Yakan lalatar da dabarun mugaye.
10 Ubangiji Sarki ne har abada!Ya Sihiyona, Allahnki zai yi mulki har dukan zamanai!Yabo Ya tabbata ga Ubangiji!