10 Ba ya jin daɗin ƙarfafan dawakai,Ba ya murna da jarumawan mayaƙa.
11 Amma yana jin daɗin waɗanda suke tsoronsa,Yana jin daɗin waɗanda suke dogara da madawwamiyar ƙaunarsa.
12 Ya Urushalima, ki yabi Ubangiji,Ya Sihiyona, ki yabi Allahnki.
13 Shi yake riƙe da ƙofofinki da ƙarfi,Yakan sa wa jama'arki albarka.
14 Yakan kiyaye kan iyakar ƙasarki lafiya,Yakan kuma ƙosar da ke da alkama mafi kyau.
15 Yakan ba da umarni,Nan da nan umarnin yakan iso duniya.
16 Yakan aiko da dusar ƙanƙara mai kauri kamar ulu,Ya watsa jaura kamar ƙura.