4 Ya ƙididdige yawan taurari,Yakan kira kowanne da sunansa.
5 Ubangijinmu mai girma ne, Mai Iko Dukka,Saninsa ya fi gaban aunawa.
6 Yakan ɗaukaka masu tawali'u,Amma yakan ragargaza mugaye har ƙasa.
7 Ku raira waƙar yabo ga Ubangiji,Ku yabi Allah da garaya.
8 Ya shimfiɗa gajimare a sararin al'arshi.Ya tanada wa duniya ruwan sama,Ya sa ciyayi su tsiro a kan tuddai.
9 Yakan ba dabbobi abincinsu,Yakan ciyar da 'ya'yan hankaki sa'ad da suka yi kuka gare shi.
10 Ba ya jin daɗin ƙarfafan dawakai,Ba ya murna da jarumawan mayaƙa.