1 Yabo ya tabbata ga Ubangiji!Ku yabi Ubangiji daga sama,Ku da kuke zaune a tuddan sama.
2 Ku yabe shi dukanku mala'ikunsa,Ku yabe shi, ku dukan rundunansa na sama!
3 Ku yabe shi, ku rana da wata,Ku yabe shi, ku taurari masu haskakawa!
4 Ku yabe shi, ku sammai mafi tsayi duka!Ku yabe shi, ku ruwayen da kuke bisa sararin sama!