3 Ku yabe shi, ku rana da wata,Ku yabe shi, ku taurari masu haskakawa!
4 Ku yabe shi, ku sammai mafi tsayi duka!Ku yabe shi, ku ruwayen da kuke bisa sararin sama!
5 Bari su duka su yabi sunan Ubangiji!Ya umarta, sai suka kasance.
6 Ta wurin umarninsa aka kafa suA wurarensu har abada,Ba su kuwa da ikon ƙi.
7 Ku yabi Ubangiji daga duniya,Ku yabi Ubangiji, ku dodanin ruwa da dukan zurfafan teku.
8 Ku yabe shi, ku walƙiya, da ƙanƙara, da dusar ƙanƙara,Da gizagizai, da ƙarfafan iska waɗanda suke biyayya da umarnansa!
9 Ku yabe shi, ku tuddai da duwatsu,Da itatuwa 'ya'ya da kurama.