6 Bari su yi sowa da ƙarfiSa'ad da suke yabon Allah, da takubansu masu kaifi.
7 Don su ci nasara bisa al'ummai,Su kuma hukunta wa jama'a,
8 Su ɗaure sarakunansu da sarƙoƙi,Su ɗaure shugabanninsu da sarƙoƙin baƙin ƙarfe,
9 Su hukunta wa al'ummai, kamar yadda Allah ya umarta.Wannan shi ne cin nasarar jama'ar Allah!Yabo ya tabbata ga Ubangiji!