1 Ya Allah, ka kiyaye ni, gama na zo gare ka neman mafaka.
2 Na ce wa Ubangiji, “Kai ne Ubangijina,Dukan kyawawan abubuwan da nake da suDaga gare ka suke.”
3 Dubi irin martabar da amintattun jama'ar Ubangiji suke da ita!Ba abin da raina ya fi so,Sai in zauna tare da su.
4 Waɗanda suke hanzari zuwa ga gumaka,Za su jawo wa kansu wahala.Ba zan yi tarayya da su da hadayarsu ba.Ba zan yi sujada ga gumakansu ba.
5 Kai ne kaɗai, nake da shi, ya Ubangiji,Kai ne kake biyan dukan bukatata,Raina yana hannunka.
6 Kyautanka zuwa gare ni da bansha'awa suke,Kyawawa ne kuwa ƙwarai!
7 Na yabi Ubangiji saboda yana bi da ni,Da dare kuma lamirina yana yi mini fadaka.