1 Don me al'ummai suke shirin tayarwa?Don me waɗannan mutane suke ƙulla shawarwarin banza?
2 Sarakunan duniya sun yi tayarwa,Masu mulkinsu suna shirya maƙarƙashiya tare,Gāba da Ubangiji da zaɓaɓɓen sarkinsa.
3 Suna cewa, “Bari mu 'yantar da kanmu daga mulkinsu,Bari mu fice daga ƙarƙashinsu!”
4 Ubangiji ya yi dariya daga kan kursiyinsa can Sama,Ya mai da su abin dariya.