4 Ubangiji ya yi dariya daga kan kursiyinsa can Sama,Ya mai da su abin dariya.
5 Ya yi musu magana da fushi,Ya razanar da su da hasalarsa,
6 Ya ce, “A bisa Sihiyona, dutsena tsattsarka,Na naɗa sarkina.”
7 Sarkin ya ce, “Zan yi shelar abin da Ubangiji ya hurta.Ubangiji ya ce mini, ‘Kai ɗana ne,Yau ne na zama mahaifinka.
8 Ka yi roƙo, zan kuwa ba ka dukan al'ummai,Dukan duniya kuma za ta zama taka.
9 Za ka mallake su da sandan ƙarfe,Za ka farfashe su kamar tukunyar yumɓu.’ ”
10 Yanzu ku kasa kunne gare ni, ku sarakuna,Ku mai da hankali, ku mahukunta!