1 Sarki yana murna, ya Ubangiji,Domin ka ba shi ƙarfi,Yana cike da farin ciki,Don ka sa ya ci nasara.
2 Ka biya masa bukatarsa,Ka amsa roƙonsa.
3 Ka zo gare shi da albarka mai yawa,Ka sa kambin zinariya a kansa.
4 Ya roƙi rai, ka kuwa ba shi mai tsawo,Da yawan kwanaki.