2 Ka biya masa bukatarsa,Ka amsa roƙonsa.
3 Ka zo gare shi da albarka mai yawa,Ka sa kambin zinariya a kansa.
4 Ya roƙi rai, ka kuwa ba shi mai tsawo,Da yawan kwanaki.
5 Darajarsa tana da girma saboda taimakonka,Ka sa ya yi suna da martaba.
6 Albarkarka tana a kansa har abada,Kasancewarka tare da shi, takan cika shi da murna.
7 Sarki yana dogara ga Maɗaukaki,Saboda madawwamiyar ƙaunar UbangijiZai zama sarki har abada.
8 Sarki zai kakkama dukan magabtansa,Zai kakkama duk waɗanda suke ƙinsa.