4 Ya roƙi rai, ka kuwa ba shi mai tsawo,Da yawan kwanaki.
5 Darajarsa tana da girma saboda taimakonka,Ka sa ya yi suna da martaba.
6 Albarkarka tana a kansa har abada,Kasancewarka tare da shi, takan cika shi da murna.
7 Sarki yana dogara ga Maɗaukaki,Saboda madawwamiyar ƙaunar UbangijiZai zama sarki har abada.
8 Sarki zai kakkama dukan magabtansa,Zai kakkama duk waɗanda suke ƙinsa.
9 Ubangiji zai hallaka su kamar harshen wuta, sa'ad da ya bayyana.Ubangiji zai cinye su a cikin fushinsa,Wuta kuma za ta cinye su ƙurmus.
10 Sarki zai karkashe 'ya'yansu duka,Zai yanyanke dukan zuriyarsu.