1 Ya Allahna, ya Allahna,Don me ka yashe ni?Na yi kuka mai tsanani, ina neman taimako,Amma har yanzu ba ka zo ba!
2 Da rana na yi kira a gare ka, ya Allahna,Amma ba ka amsa ba.Da dare kuma na yi kira,Duk da haka ban sami hutawa ba.
3 Amma an naɗa ka Mai Tsarki,Wanda Isra'ila suke yabonsa.
4 Kakanninmu suka dogara gare ka,Sun dogara gare ka, ka kuwa cece su.
5 Suka yi kira gare ka, suka tsira daga hatsari,Suka dogara gare ka, ba su kuwa kunyata ba.
6 A yanzu dai ni ba mutum ba ne, tsutsa ne kawai,Rainanne, abin ba'a ga kowa da kowa!
7 Duk wanda ya gan niSai yă maishe ni abin dariya,Suna zunɗena da harshensu suna kaɗa kai.