18 Suka rarraba tufafina a tsakaninsu,Suka jefa kuri'a a kan babbar rigata.
19 Kada ka yi nisa da ni, ya Ubangiji!Ka gaggauta ka cece ni, ya Mai Cetona!
20 Ka cece ni daga takobi,Ka ceci raina daga waɗannan karnuka.
21 Ka kuɓutar da ni daga waɗancan zakoki,Ba ni da mataimaki a gaban bijimai masu mugun hali.
22 Zan faɗa wa mutanena abin da ka yi,Zan yabe ka cikin taronsu.
23 “Ku yabe shi, ku bayin Ubangiji!Ku girmama shi, ku zuriyar Yakubu!Ku yi masa sujada, ku jama'ar Isra'ila!
24 Ba ya ƙyale matalauta,Ko ya ƙi kulawa da wahalarsu,Ba ya rabuwa da su,Amma yakan amsa lokacin da suka nemi taimako.”