3 Amma an naɗa ka Mai Tsarki,Wanda Isra'ila suke yabonsa.
4 Kakanninmu suka dogara gare ka,Sun dogara gare ka, ka kuwa cece su.
5 Suka yi kira gare ka, suka tsira daga hatsari,Suka dogara gare ka, ba su kuwa kunyata ba.
6 A yanzu dai ni ba mutum ba ne, tsutsa ne kawai,Rainanne, abin ba'a ga kowa da kowa!
7 Duk wanda ya gan niSai yă maishe ni abin dariya,Suna zunɗena da harshensu suna kaɗa kai.
8 Suka ce, “Ka dogara ga Ubangiji,Me ya sa bai cece ka ba?Idan Ubangiji na sonka,Don me bai taimake ka ba?”
9 Kai ne ka fito da ni lafiya a lokacin da aka haife ni,A lokacin da nake jariri ka kiyaye ni.