1 Duniya da dukan abin da yake cikinta na Ubangiji ne,Duniya da dukan mazaunanta nasa ne.
2 Ya gina ta a bisa ruwa mai zurfi na ƙarƙashin ƙasa,Ya kuma kafa harsashinta a zurfin teku.
3 Wa yake da iko yă hau tudun Ubangiji?Wa yake da iko ya shiga Haikalinsa tsattsarka?
4 Sai wanda yake da tsarki cikin aiki, da tunani,Wanda ba ya yi wa gumaka sujada,Ko kuma yă yi alkawarin ƙarya.
5 Ubangiji zai sa masa albarka,Allah Mai Cetonsa zai kuɓutar da shi.
6 Su ne irin mutanen da suke zuwa wurin Allah,Waɗanda suke zuwa a gaban Allah na Yakubu.