5 Ubangiji zai sa masa albarka,Allah Mai Cetonsa zai kuɓutar da shi.
6 Su ne irin mutanen da suke zuwa wurin Allah,Waɗanda suke zuwa a gaban Allah na Yakubu.
7 A buɗe ƙofofi sosai,A buɗe daɗaɗɗun ƙofofi,Babban Sarki kuwa zai shigo!
8 Wane ne wannan babban Sarki?Ubangiji ne mai ƙarfi mai iko,Ubangiji mai nasara cikin yaƙi!
9 A buɗe ƙofofi sosai,A buɗe daɗaɗɗun ƙofofi,Babban Sarki kuwa zai shigo!
10 Wane ne wannan babban Sarki?Ubangiji Mai Runduna, shi ne babban Sarki!