1 A gare ka nake yin addu'a, ya Ubangiji,
2 A gare ka nake dogara, ya Allah.Ka cece ni daga shan kunyar fāɗuwa,Kada ka bar magabtana su yi mini duban wulakanci!
3 Waɗanda suke dogara gare ka,Ba za su kasa yin nasara ba,Sai dai waɗanda suke gaggawa su yi maka tayarwa.
4 Ka koya mini al'amuranka, ya Ubangiji,Ka sa su zama sanannu a gare ni.
5 Ka koya mini in yi zamana bisa ga gaskiyarka,Gama kai Mai Cetona ne.Dukan yini ina dogara a gare ka.
6 Ya Ubangiji, ka tuna da alherinka da madawwamiyar ƙaunarka,Waɗanda ka nuna tun a dā.
7 Ka gafarta zunubaina da kurakuraina masu yawa na ƙuruciyata.Saboda madawwamiyar ƙaunarka da alherinka,Ka tuna da ni, ya Ubangiji!