11 Ka cika alkawarinka, ya Ubangiji, ka gafarta zunubaina, gama suna da yawa.
12 Waɗanda suke biyayya da UbangijiZa su koyi hanyar da za su bi daga gare shi.
13 Kullayaumi za su arzuta,'Ya'yansu kuma za su zauna lafiya a ƙasar.
14 Ubangiji yakan amince da waɗanda suke biyayya da shi,Yakan koya musu alkawarinsa.
15 A koyaushe ga Ubangiji nake neman taimako,Yakan kuɓutar da ni daga hatsari.
16 Ka juyo wajena, ya Ubangiji, ka yi mini jinƙai,Gama ina zaman kaɗaici da rashin ƙarfi.
17 Damuwar zuciyata ta yi yawa,Ka raba ni da dukan damuwa,Ka cece ni daga dukan wahalata.