17 Damuwar zuciyata ta yi yawa,Ka raba ni da dukan damuwa,Ka cece ni daga dukan wahalata.
18 Ka kula da wahalata da azabata,Ka gafarta dukan zunubaina.
19 Ka duba yawan magabtan da nake da su,Dubi irin ƙiyayyar da suke yi mini!
20 Ka yi mini kāriya, ka cece ni,Gama na zo wurinka neman kāriya.
21 Ka sa nagartata da amincina su kiyaye ni,Gama na dogara gare ka.
22 Ka fanshi jama'arka daga dukan wahalarsu, ya Allah!