7 Ka gafarta zunubaina da kurakuraina masu yawa na ƙuruciyata.Saboda madawwamiyar ƙaunarka da alherinka,Ka tuna da ni, ya Ubangiji!
8 Ubangiji mai adalci ne, mai alheri,Yana koya wa masu zunubi tafarkin da za su bi.
9 Yana bi da masu tawali'u a tafarkin da suke daidai,Yana koya musu nufinsa.
10 Da ƙauna da aminci yana bi da dukan waɗanda suke biyayya da alkawarinsa da umarnansa.
11 Ka cika alkawarinka, ya Ubangiji, ka gafarta zunubaina, gama suna da yawa.
12 Waɗanda suke biyayya da UbangijiZa su koyi hanyar da za su bi daga gare shi.
13 Kullayaumi za su arzuta,'Ya'yansu kuma za su zauna lafiya a ƙasar.