1 Ka hurta rashin laifina, ya Ubangiji,Gama na yi abin da suke daidai,Na dogara gare ka gaba ɗaya.
2 Ka jarraba ni ka auna ni, ya Ubangiji,Ka gwada muradina da tunanina.
3 Madawwamiyar ƙaunarka tana bi da ni,Amincinka yake yi mini jagora kullayaumin.
4 Ba na tarayya da mutanen banza,Ba abin da ya gama ni da masu riya.