1 Na zo gare ka, ya Ubangiji, domin ka kiyaye ni.Kada ka bari a yi nasara da ni.Kai Allah mai adalci ne,Ka cece ni, ina roƙonka!
2 Ka ji ni! Ka cece ni yanzu!Ka zama mafakata, don ka kiyaye ni,Ka zama mai kāre ni, don ka cece ni.
3 Kai ne mafakata da kariyata,Ka bi da ni yadda ka alkawarta.
4 Ka kiyaye ni daga tarkon da aka kafa domina,Kai ne inuwata.
5 Ina ba da kaina gare ka domin ka kiyaye ni.Za ka fanshe ni, ya Ubangiji,Kai Allah mai aminci ne.
6 Kana ƙin waɗanda suke yi wa gumaka sujada,Amma ni na dogara gare ka.